Hadith for the World
Fiqihun Halaye

Munanan Halaye

21 hadiths

21 hadiths

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Hurairah, yardar Allah ta tabbata a gare shi, tare da rahoto kan mai zuwa: “Shin kun san wanda ya bankare?” Suka ce: Fatara tana daga cikinmu wanda ba shi da kudi ko kaya, sai ya ce: “Fatarar daga al’ummata ita ce wani wanda ya zo ranar tashin kiyama da salla, da azumi da zakka, sai ya zo aka zagi wannan, wannan kuma aka jefa shi, kuma ya cinye wannan kudin, kuma wannan jini ya zube, kuma wannan an buge shi, kuma ana bayar da wannan ne daga kyawawan ayyukansa. Wannan yana daga cikin kyawawan ayyukansa. Idan kyawawan ayyukansa suka baci kafin a biya shi hakinsa, zai dauke zunubansu sai a jefa shi, sa'annan a jefa shi cikin Wuta. ”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ibn Umar - Allah ya yarda da su - tare da rubutun: "Zalunci duhu ne a ranar tashin kiyama." Daga Jaber - Allah ya yarda da su - a cikin rahoton marfoo: “Ku kiyayi zalunci, domin zalunci duhu ne a ranar tashin kiyama, kuma ku kiyayi karanci. Domin ta halakar da wanda ya gabace ka. ”Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance, kada ku yi binciken (aibobin mutane), kada ku yi hassada, kada kujuyawa juna baya, kada ku yi kiyayya, ku zama bayin Allah 'yan uwa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bn Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Daya daga cikin manyan zunubai shi ne mutum ya zagi iyayensa." Aka ce: Shin mutumin yana zagin iyayensa ne? Sai ya ce: Ee, ya zagi mahaifin mutum, ya zagi mahaifinsa, mahaifiyarsa kuma ta zagi mahaifiyarsa.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inciBukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم ، قَالَ: «لا يدخلُ الجنةَ مَن كان في قلبه مِثقال ذرةٍ من كِبر» فقال رجل: إنّ الرجلَ يحب أن يكون ثوبه حسنا، ونَعله حسنة؟ قال: «إنّ الله جميلٌ يحب الجمالَ، الكِبر: بَطَرُ الحق وغَمْطُ الناس».رواه مسلم
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din sa
Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَرَّ عَلَى صُبْرَةِ طَعَامٍ فَأَدْخَلَ يَدَهُ فِيهَا، فَنَالَتْ أَصَابِعُهُ بَلَلًا فَقَالَ: «مَا هَذَا يَا صَاحِبَ الطَّعَامِ؟» قَالَ أَصَابَتْهُ السَّمَاءُ يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «أَفَلَا جَعَلْتَهُ فَوْقَ الطَّعَامِ كَيْ يَرَاهُ النَّاسُ؟ @مَنْ غَشَّ فَلَيْسَ مِنِّي».رواه مسلم