Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:

Available in 40 languages
«Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - ya wuce wasu manoma daga baubayi a Sham, an tsayar da su a zafin rana, sai ya yi tambaya game da lamarinsu? Sai aka ba shi labarin cewa su an aikata musu haka ne saboda basu bada (jizya ba) alhali su suna da ikon hakan. Sai Hisham - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ina shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya akan zalinci ba tare da wani haƙƙi ba.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality