Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 43 languages
«Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality