Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:

Available in 60 languages
«Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.

Source
Bukhari ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality