Hadith for the World
FALALOLI DA LADUBBA

Fiqihun Halaye

56 hadiths

56 hadiths

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi
Abu Musa al-Ash'ari Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi: «Tsoron Allah Madaukaki: Girmama Musulmin Shaiba, kuma mai riko da Kur'ani yana da daraja a ciki, kuma ya bushe shi, da girmamawa tare da Sultan spondylitis».Abu Daud Ya Rawaito shi
Daga Abu Hurairah, yardar Allah ta tabbata a gare shi, tare da rahoto kan mai zuwa: “Shin kun san wanda ya bankare?” Suka ce: Fatara tana daga cikinmu wanda ba shi da kudi ko kaya, sai ya ce: “Fatarar daga al’ummata ita ce wani wanda ya zo ranar tashin kiyama da salla, da azumi da zakka, sai ya zo aka zagi wannan, wannan kuma aka jefa shi, kuma ya cinye wannan kudin, kuma wannan jini ya zube, kuma wannan an buge shi, kuma ana bayar da wannan ne daga kyawawan ayyukansa. Wannan yana daga cikin kyawawan ayyukansa. Idan kyawawan ayyukansa suka baci kafin a biya shi hakinsa, zai dauke zunubansu sai a jefa shi, sa'annan a jefa shi cikin Wuta. ”Muslim ne ya rawaito shi
Dag Mu'az -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Duk wanda ya haxiye fushi, kuma yana da ikon ya ya rama, Allah zai kirawo shi a cikin Mutane a Ranar Al-qiyama ya zava Masa daga cikin Matan Hurul-Aini abunda ya so"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Lallai, Allah madaukaki yana cewa a ranar kiyama: Ina wadanda suke kauna a cikin Mai girma na? A yau zan yi musu inuwa a cikin inuwa ta, rana babu wata inuwa sai tawa. ”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «جَعَلَ اللهُ الرحمةَ مائة جُزْءٍ، فَأَمْسَكَ عِنْدَهُ تِسْعَةً وَتِسْعِينَ، وأَنْزَلَ في الأَرْضِ جُزْءًا وَاحِدًا، فَمِنْ ذَلِكَ الجُزْءِ يَتَرَاحَمُ الخَلَائِقُ، حتى تَرْفَعَ الدَّابَّةُ حَافِرَهَا عَنْ وَلَدِهَا خَشْيَةَ أَنْ تُصِيبَهُ». وفي رواية «إِنَّ للهِ تعالى مئةُ رحمةٍ، أَنْزَلَ منها رحمةً واحدةً بَيْنَ الجِنِّ والإنسِ والبَهَائِمِ والهَوَامِّ، فَبِهَا يَتَعَاطَفُونَ، وبها يَتَرَاحَمُونَ، وبِهَا تَعْطِفُ الوَحْشُ على وَلَدِهَا، وأَخَّرَ اللهُ تعالى تِسْعًا وتِسْعِينَ رحمةً يَرْحَمُ بِهَا عِبَادَهُ يومَ القِيَامَةِ». وعن سلمان الفارسي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إِنَّ للهِ تعالى مئةُ رحمةٍ فمنها رحمةٌ يَتَرَاحَمُ بها الخَلْقُ بَيْنَهُمْ، وتِسْعٌ وتِسْعُونَ لِيَومِ القِيَامَةِ». وفي رواية: «إِنَّ اللهَ تَعَالَى خَلَقَ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ والأَرْضَ مئةَ رحمةٍ كُلُّ رحمةٍ طِبَاقَ مَا بَيْنَ السَّمَاءِ إلى الأَرْضِ، فَجَعَلَ منها في الأَرْضِ رَحْمَةً فبها تَعْطِفُ الوَالِدَةُ على وَلَدِهَا، والوَحْشُ والطَّيْرُ بَعْضُهَا عَلَى بَعْضٍ، فإذا كانَ يومُ القيامةِ أَكْمَلَهَا بِهَذِه الرحمةِ».حديث أبي هريرة -رضي الله عنه-: متفق عليه. حديث سلمان -رضي الله عنه-: رواه مسلم
Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Nawwas ɗan Sam'an alAnsari - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa Musulmi, kowane Musulmi akan Musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Bai Kamata Musulmi ya zamanto mai yawan tsinuwa ba"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri".Muslim ne ya rawaito shi
Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: Ina tafiya tare da Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuma ta sanyin sawun Najrani mai kauri, Fjbzh Bedouin riguna, sanya shi Jbzh mai tsanani, na duba shafin da ke kwance tare da Annabi aminci ya tabbata a gare shi, ya shafi rigar sawun kafa Da karfi ya ja shi, sannan ya ce: Ya Muhammad, ka bar ni daga kudin Allah da kake da su. sannan ya juyo gare shi, ya yi dariya, sannan ya yi masa umarni da kyauta.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ibn Umar - Allah ya yarda da su - tare da rubutun: "Zalunci duhu ne a ranar tashin kiyama." Daga Jaber - Allah ya yarda da su - a cikin rahoton marfoo: “Ku kiyayi zalunci, domin zalunci duhu ne a ranar tashin kiyama, kuma ku kiyayi karanci. Domin ta halakar da wanda ya gabace ka. ”Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance, kada ku yi binciken (aibobin mutane), kada ku yi hassada, kada kujuyawa juna baya, kada ku yi kiyayya, ku zama bayin Allah 'yan uwa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni: "Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska".Muslim ne ya rawaito shi