Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas bin Malik - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Duk wanda ya ce - ma’ana: idan ya fita daga gidansa -: Da sunan Allah na dogara ga Allah, kuma babu wani karfi ko iko sai ga Allah, za a ce masa: Ka shiryu, ka isa, kuma ka yi albarka.” Abu Dawud ya kara da cewa: "Sai ya ce - ma'anarsa: Shaidan - ga wani shaidan: Ta yaya za ku sami mutumin da ya shiryu, ya isa, kuma ya tsare?"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi
Daga Muadh bn Jabal - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan manzon Allah - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: "Allah mai girma da daukaka ya ce: Wadanda suka yi ni'ima a cikin Jalali suna da ayoyin haske da annabawa da shahidai za su so."Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra da Ibnu Majah ne Suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Katadah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bin Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah na gafarta wa shahidi komai sai addini." Kuma a cikin wata ruwaya daga gare shi cewa: “Kisa a cikin tafarkin Allah yana kankare komai face addini.”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».Muslim ne ya rawaito shi
عن أبي هريرة، عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إن العبد لَيَتَكَلَّمُ بالكلمة من رِضْوَانِ الله تعالى ما يُلْقِي لها بَالًا يَرْفَعُهُ الله بها درجاتٍ، وإن العبد لَيَتَكَلَّمُ بالكلمة من سَخَطِ الله تعالى لا يُلْقِي لها بَالًا يَهْوِي بها في جهنم». وعن أبي عبد الرحمن بلال بن الحارث المزني رضي الله عنه : أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إن الرجل لَيَتَكَلَّمُ بالكلمة من رِضْوَانِ الله تعالى ما كان يظن أن تبلغ ما بَلَغَتْ يكتب الله له بها رِضْوَانَهُ إلى يوم يَلْقَاهُ، وإن الرجل لَيَتَكَلَّمُ بالكلمة من سَخَطِ الله ما كان يظن أن تبلغ ما بَلَغَتْ يكتب الله له بها سَخَطَهُ إلى يوم يَلْقَاهُ».حديث أبي هريرة -رضي الله عنه-: رواه البخاري. حديث بلال المزني -رضي الله عنه-: رواه الترمذي وابن ماجه ومالك وأحمد
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai matakai dari a cikin Aljanna da Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin sahu biyu kamar tsakanin sama da kasa."Buhari ne ya rawaito shi
عن جابر رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إن في الليل لساعة، لا يُوَافِقُهَا رجُلٌ مُسلم يَسأل الله تعالى خيرًا من أمْرِ الدنيا والآخرة، إلا أعْطَاه إِياه، وذلك كُلَّ ليلة».رواه مسلم
عن أبي هريرة رضي الله عنه : أن رجلًا أتى النبي صلى الله عليه وسلم يَتَقَاضَاهُ فَأغْلَظَ له، فَهَمَّ به أصحابه، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «دَعُوه، فإن لِصَاحب الحَقِّ مَقَالا» ثم قال: «أعْطُوهُ سِنًّا مِثْل سِنِّهِ» قالوا: يا رسول الله، لا نَجِدُ إلا أمْثَلَ مِنْ سِنِّهِ، قال: «أعْطُوه، فإن خَيْرَكم أحْسَنُكُم قَضَاء».متفق عليه
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Shuraih ɗan Hani'i ya ce: Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki.Muslim ne ya rawaito shi