HA
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA
Bincike da ya game komai na Qur’ani
3 hadiths
Hukunce Hukunce Al-qur’ani
1
Ladaban Karanta Al-qur’ani da kuma Haddace shi
2
3 hadiths
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jundubu Bn Abdullahi -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Ku karanta Al-qur'ani abunda zukatanku suka fahimta, to idan kuma kuka sava to ku tashi ku barshi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi