Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 43 languages
«Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta wanda ya karanta Alƙur'ani kuma ya saba da karanta shi - daidai ne yana dubawa daga Mushafi ne ko da ka yake yi - da ma'abocin dabaibayayyun raƙuma da igiyar da ake ɗaure gwiwowin raƙuma da su, idan ya kula sai ya ci gaba da riƙesu, idan kuma ya saki ɗaurinsu sai su tafi su suɓuce, idan ma'abocin Alƙur'ani ya tsaya sai ya karanta shi zai tuna shi, idan kuma bai tsayu da shi ba to zai manta shi; lazimta ba zata gushe tana samammiya ba sai hadda itama ta zama tana nan.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality