Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 65 languages
«Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality