Hadith for the World
Fiqihun Addu'o'i da Zikiri

Zikirin Safiya da Maraice

4 hadiths

4 hadiths

A kan Abdullahi bin Masoud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabin Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: “Mun zauna, kuma sarki ya kasance na Allah ne. "Sarki yana gare shi kuma a gare shi yabo ne, kuma yana iya yin komai. Bari in roke ku mafificin wannan daren da kuma mafi alherin da ke zuwa bayan haka, kuma ina neman tsarinku daga sharrin abin da ke wannan daren da kuma sharrin abin da ke zuwa. Kuma azaba a cikin kabari. "Kuma idan ya zama, ya kuma faɗi cewa," Mun zama kuma sarki ya zama Allah. "Muslim ne ya rawaito shi
Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai". ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi