Hadith for the World
Fiqihun Addu'o'i da Zikiri

Zikiri da ba su da wani Qaidi

5 hadiths

5 hadiths

Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra da Ibnu Majah ne Suka rawaito shi
Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.Muslim ne ya rawaito shi
عَنْ أَبِي مَالِكٍ الْأَشْجَعِيُّ عَنْ أَبِيهِ قَالَ: كَانَ الرَّجُلُ إِذَا أَسْلَمَ عَلَّمَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الصَّلَاةَ، ثُمَّ أَمَرَهُ أَنْ يَدْعُوَ بِهَؤُلَاءِ الْكَلِمَاتِ: «اللهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَاهْدِنِي وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي». وَفِي رِوَايَةٍ: أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَتَاهُ رَجُلٌ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ كَيْفَ أَقُولُ حِينَ أَسْأَلُ رَبِّي؟ قَالَ: «قُلْ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي» وَيَجْمَعُ أَصَابِعَهُ إِلَّا الْإِبْهَامَ «فَإِنَّ هَؤُلَاءِ تَجْمَعُ لَكَ دُنْيَاكَ وَآخِرَتَكَ».رواه مسلم