Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 65 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne: "Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya. "Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi. "Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality