Hadith for the World
Fiqihun Addu'o'i da Zikiri

Koyarwar Manzon Allah SAW a cikin Zikiri

5 hadiths

5 hadiths

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaice
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «وَاللهِ إني لأَسْتَغْفِرُ اللهَ وأَتُوبُ إليهِ في اليومِ أَكْثَرَ من سَبْعِينَ مَرَّةً».رواه البخاري
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".Muslim ne ya rawaito shi