Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 49 languages
«Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya haddace ayoyi goma a zahirin zuciya (hadda) daga farkon Suratul Kahf za'a tsare shi za'a kare shi daga fitinar Masihul Dajjal wanda zai fito a ƙarshen zamani kuma zai yi da'awar Uluhiyya (Allantaka), kuma fitinarsa ita ce mafi girman fitinar da za ta kasance a kan ƙasa tun lokacin da aka halicci (annabi) Adam har zuwa tashin alƙiyama; saboda abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai tabbatar masa daga sashin al'amura masu saɓa hankali waɗanda zai fitini wanda ya bi shi, hakan domin cewa farkon Suratul Kahf a cikinta akwai abubuwan mamaki da ayoyi abinda yake yafi girma daga abinda Dujal zai fitini mutane a cikinsa, wanda ya yi tuntuntuni to ba za'a fitina shi da Dujjal ba. A cikin wata riwayar: Ayoyi goma daga ƙarshen surar daga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Shin waɗanda suka kafirta suna zatan zasu riƙi...}.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality