HA
Imani da Ranar Lahira
Alamomin tashin Al-qiyama
4 hadiths
Rayuwar Barzahu
2
Alamomin tashin Al-qiyama
4
Rayuwar Lahira
15
4 hadiths
Daga Mirdas Al-Aslami, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: “Masu adalci na farko sun tafi na farkon, kuma tabo ya kasance kamar sha’ir ko dabino.
Buhari ne ya rawaito shi
Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: "A iyakokin Madina Mala'iku Annoba da Dujal basa shigar ta"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi