Hadith for the World
Imani da Ranar Lahira

Rayuwar Lahira

15 hadiths

15 hadiths

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Dag Mu'az -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Duk wanda ya haxiye fushi, kuma yana da ikon ya ya rama, Allah zai kirawo shi a cikin Mutane a Ranar Al-qiyama ya zava Masa daga cikin Matan Hurul-Aini abunda ya so"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Lallai, Allah madaukaki yana cewa a ranar kiyama: Ina wadanda suke kauna a cikin Mai girma na? A yau zan yi musu inuwa a cikin inuwa ta, rana babu wata inuwa sai tawa. ”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Muadh bn Jabal - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan manzon Allah - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: "Allah mai girma da daukaka ya ce: Wadanda suka yi ni'ima a cikin Jalali suna da ayoyin haske da annabawa da shahidai za su so."Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai matakai dari a cikin Aljanna da Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin sahu biyu kamar tsakanin sama da kasa."Buhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: "Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Lallai kafiri idan ya aikata Kyakkyawan aiki, sai a ciyar da shi Abinci a Duniya, Kuma Mumini Saboda Allah yana masa tanadin Kyawawan lada a Lahira, kuma ya bibiye shi da arziki a cikin Duniya kan biyayyarsa"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Mu'awiya -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba: "Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci, domin ni na ji takun takalmanka a gabana a cikin aljanna" Ya ce: Ban taɓa aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a gurina sai dai cewa bana yin wata alwala a lokacin dare ko rana, sai na sallaci abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ، وَأَقَامَ الصَّلاَةَ، وَصَامَ رَمَضَانَ كَانَ حَقًّا عَلَى اللَّهِ أَنْ يُدْخِلَهُ الجَنَّةَ، جَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوْ جَلَسَ فِي أَرْضِهِ الَّتِي وُلِدَ فِيهَا»، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَلاَ نُبَشِّرُ النَّاسَ؟ قَالَ: «إِنَّ فِي الجَنَّةِ مِائَةَ دَرَجَةٍ، أَعَدَّهَا اللَّهُ لِلْمُجَاهِدِينَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، مَا بَيْنَ الدَّرَجَتَيْنِ كَمَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، فَإِذَا سَأَلْتُمُ اللَّهَ فَاسْأَلُوهُ الفِرْدَوْسَ، فَإِنَّهُ أَوْسَطُ الجَنَّةِ وَأَعْلَى الجَنَّةِ -أُرَاهُ- فَوْقَهُ عَرْشُ الرَّحْمَنِ، وَمِنْهُ تَفَجَّرُ أَنْهَارُ الجَنَّةِ».رواه البخاري