Hadith for the World
ILIMIN AƘIDA

Imani da Ranar Lahira

26 hadiths

26 hadiths

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mirdas Al-Aslami, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: “Masu adalci na farko sun tafi na farkon, kuma tabo ya kasance kamar sha’ir ko dabino.Buhari ne ya rawaito shi
Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Dag Mu'az -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Duk wanda ya haxiye fushi, kuma yana da ikon ya ya rama, Allah zai kirawo shi a cikin Mutane a Ranar Al-qiyama ya zava Masa daga cikin Matan Hurul-Aini abunda ya so"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Lallai, Allah madaukaki yana cewa a ranar kiyama: Ina wadanda suke kauna a cikin Mai girma na? A yau zan yi musu inuwa a cikin inuwa ta, rana babu wata inuwa sai tawa. ”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Muadh bn Jabal - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan manzon Allah - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: "Allah mai girma da daukaka ya ce: Wadanda suka yi ni'ima a cikin Jalali suna da ayoyin haske da annabawa da shahidai za su so."Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai matakai dari a cikin Aljanna da Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin sahu biyu kamar tsakanin sama da kasa."Buhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Jabir Bn Abdullah -Allah ya yarda da su- "Kowane bawa za a tayar da shi ranar tashin kiyama a cikin yanayin da ya mutu. a kansa"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: "Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Lallai kafiri idan ya aikata Kyakkyawan aiki, sai a ciyar da shi Abinci a Duniya, Kuma Mumini Saboda Allah yana masa tanadin Kyawawan lada a Lahira, kuma ya bibiye shi da arziki a cikin Duniya kan biyayyarsa"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Mu'awiya -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: "A iyakokin Madina Mala'iku Annoba da Dujal basa shigar ta"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice, idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna ne to yana daga cikin 'yan aljanna, idan ya kasance daga cikin 'yan wuta to yana daga cikin 'yan wuta, sai a ce: Wannan mazauninka ne har sai Allah Ya tasheka ranar alƙiyama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu, wannan yayin da: {Wani rai imanin sa ba zai anfane shi ba, bai yi imani ba kafin nan, ko bai aikata alheri a imanin na sa ba} [Al-An'am: 158] kuma lalli Alkiyama za ta tsaya alhali mutum biyu za su shinfida tufafinsu a tsakaninsu ba za su saida shi ba, ba kuma za su ninkeshi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali hakika mutum ya juya da nonon taguwarsa da ta tatsa ba zai dandane shi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali shi yana yabe tafkinsa ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tsaya alhali hakika dayanku ya daga lomarsa zuwa bakinsa ba zai cinyeta ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".Muslim ne ya rawaito shi