Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa;

Available in 55 languages
«Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality