Hadith for the World
Azumi

Falalar Azumi

5 hadiths

5 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها قالت: دخل علي النبي صلى الله عليه وسلم ذات يوم فقال: «هل عندكم شيء؟» فقلنا: لا. قال: «فإني إذن صائم» ثم أتانا يومًا آخر فقلنا: يا رسول الله، أهدي لنا حيس. فقال: «أَرِينيه، فلقد أصبحت صائمًا» فأكل.رواه مسلم