HA
ILIMIN AƘIDA
Jivanta da Barranta
4 hadiths
Hukunce Hukunce jivanta da barranta
2
Kamanceceniyar da aka Haramta
1
Al-hajar da Sharaxansa
1
4 hadiths
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
Nasa'i ya rawaito shi cikin Alkubra da Ibnu Majah da ma'anarsa haka kuma Ahmad suka ruwaito shi