Hadith for the World
Imani da Manzanni

Annabinmu Muhammad SAW

7 hadiths

7 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi", suka ce: ya Manzon Allah, wa zai ƙi? ya ce: "Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya saɓa min to haƙiƙa ya ƙi".Bukhari ne ya rawaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه : أنّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُتِيَ لَيْلَةَ أُسْرِيَ بِهِ بِقَدَحَيْنِ مِنْ خَمْرٍ وَلَبَنٍ، فَنَظَرَ إِلَيْهمَا فَأَخَذَ اللَّبَنَ. فَقَالَ جِبريل: الحَمْدُ للهِ الَّذِي هَدَاكَ لِلفِطْرَةِ لَوْ أخَذْتَ الخَمْرَ غَوَتْ أُمَّتُكَ.متفق عليه
Daga Wasila bn Al-asqa'a -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai Allah ya Zavi Kinanata daga cikin 'ya'yan Isma'il, kuma ya zavi Quraishawa daga cikin Kinanata, kuma ya zavi bani Hashim daga cikin Quraishawa, kuma ya zavoni daga cikin Bani hashim, saboda haka mi me Shugaban "yan Adam kuma babu Al-fahari, kuma ni ne farkon wanda Qasa zata keto masa, kuma farkon Mai ceto kuma farkon wanda za'a ceta"Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi
Daga Abu Musa Al'ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce:Manzon Allah SAW ya gaya mana wasu sunayaensa wasu daga ciki mun riqe, sai ya ce: "Ni Muhammad da Ahmad da Al-muqaffa, da Al-hashir, da Annabin rahama" Yazid ya ce: da Annabin Tuba da Annabin Yaqi"Ahmad ne ya rawaito shi - Muslim ne ya rawaito shi
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مِنْ أَشَدِّ أُمَّتِي لِي حُبًّا نَاسٌ يَكُونُونَ بَعْدِي، يَوَدُّ أَحَدُهُمْ لَوْ رَآنِي بِأَهْلِهِ وَمَالِهِ».رواه مسلم