Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 54 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa: Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka. Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality