Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce :

Available in 71 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta, kuma a cikinta sakayyar aikinsa take, to, imaninsa zai kwaɗaitar da shi a kan aikata waɗannan ɗabi'un. Na farko: Magana mai kyau: Ta tasbihi da hailala, da horo da aikin alheri, da hani daga abin ƙi, da gyara a tsakaknin mutane, idan bai aikata ba, to, ya lazimci shiru, ya kame daga cutarwa, ya kiyaye harshensa. Na biyu: Girmama maƙoci: Da kyautata masa da rashin cutar da shi. Na uku: Girmama baƙo mai gabatowa don ziyararka: Ta hanyar daddaɗan zance da ciyar da abinci da makamancin hakan.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality