Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce:

Available in 41 languages
«Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin gidansa kuma me yake aikatawa? Sai ta ce: Ya kasance mutum ne daga cikin mutane, yana aikata abinda maza suke aikatawa a cikin gidajensu, sai ya kasance a cikin hidimar kansa da iyalansa; yana tatsar nonon akuyarsa, yana ɗinke tufafinsa, yana gyara takalminsa, yana ɗinke gugansa, kuma ya kasance idan lokacin tada sallah ya yi sai ya fita zuwa gareta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba tare da wani jinkiri ba.

Source
Bukhari ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality