Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:

Available in 60 languages
«Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu wani musulmin da lokacin sallar farilla zai shigo masa, sai ya kyautata alwalarta, ya cikata, sannan ya yi khushu'i a sallarsa ta inda zuciyarsa da gabbansa gaba dayansu zasu zama masu fuskantar Allah masu halarto girmansa, kuma ya cika ayyukan sallah kamar ruku'u da sujjada da waninsa, sai ta zama mai kankarewa ce ga abinda ke gabanta na kananan zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi daga manyan laifuka ba, wannan falalar mai mikewa ce iya shudewar zamani kuma a kowacce sallah.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality