Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 70 languages
«Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa, za’a ce da makarancin Alkur’ani, mai aiki da abinda ke cikinsa, wanda ya lazimceshi a karatu da hadda idan ya shiga Aljanna: Ka karanta ka daukaka da wannan a cikin darajojin Aljanna, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya da karanta shi da bi ahankali da nutsuwa; domin cewa matsayinka na karshen ayar da ka karantata ne.

Source
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi
Download image

Saved at original quality