HA
All hadiths
The complete card collection, filter by chapter
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA
26
HADISI DA ILIMANSA
3
ILIMIN AƘIDA
135
FIƘHU DA USULU
288
FALALOLI DA LADUBBA
288
DA'AWA DA HISBA
15
SIRA DA TARIHI
38
655 hadiths
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Alah Ya yarda da shi - ya ce: Ya ji Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Da a ce za ku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro, da Ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace kuma ya yi yammaci a ƙoshe".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
Muslim ne ya rawaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «وَاللهِ إني لأَسْتَغْفِرُ اللهَ وأَتُوبُ إليهِ في اليومِ أَكْثَرَ من سَبْعِينَ مَرَّةً».
رواه البخاري
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci. Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku. Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku. Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku. Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku. Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi. Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".
Tirmizi ne ya ruwaito shi
عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم :«عُرِضَتْ عَلَيَّ أعمالُ أُمتي، حَسَنُهَا وسَيِّئُهَا فَوَجَدتُ في مَحَاسِنِ أَعْمَالِهَا الأَذَى يُمَاطُ عَنِ الطَّرِيقِ، ووَجَدتُ في مَسَاوِئِ أَعْمَالِهَا النُّخَاعَةُ تَكُونُ في المَسْجِدِ لا تُدْفَنُ».
رواه مسلم
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أبي أمامة رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم كَانَ إذا رَفَعَ مَائِدَتَهُ، قال: «الحَمْدُ للهِ حَمْدًا كَثِيرًا طَيِّبًا مُبَارَكًا فِيهِ، غَيْرَ مَكْفِيٍّ، وَلَا مُوَدَّعٍ، وَلَا مُسْتَغْنًى عَنْهُ رَبَّنَا».
رواه البخاري
A kan A’isha, yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta ce: Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.
Muslim ne ya rawaito shi
عن عائشة رضي الله عنها والمغيرة بن شعبة رضي الله عنه : أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يقوم من الليل حتى تَتَفَطَّرَ قَدَمَاهُ فقلت له: لم تَصْنَعُ هذا يا رسول الله، وقد غفر اللهُ لك ما تقدم من ذنبك وما تأخر؟ قال: «أَفَلَا أحب أن أكونَ عبدا شَكُورًا».
حديث عائشة -رضي الله عنها-: متفق عليه. حديث المغيرة بن شعبة -رضي الله عنه-: متفق عليه
Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Bai Kamata Musulmi ya zamanto mai yawan tsinuwa ba"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri".
Muslim ne ya rawaito shi
Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: Ina tafiya tare da Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuma ta sanyin sawun Najrani mai kauri, Fjbzh Bedouin riguna, sanya shi Jbzh mai tsanani, na duba shafin da ke kwance tare da Annabi aminci ya tabbata a gare shi, ya shafi rigar sawun kafa Da karfi ya ja shi, sannan ya ce: Ya Muhammad, ka bar ni daga kudin Allah da kake da su. sannan ya juyo gare shi, ya yi dariya, sannan ya yi masa umarni da kyauta.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi", suka ce: ya Manzon Allah, wa zai ƙi? ya ce: "Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya saɓa min to haƙiƙa ya ƙi".
Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Lokacin da Allah ya halicci halitta, ya rubuta a cikin wani littafi, kuma yana tare da shi a kan karaga: Rahamata ta rinjayi fushina." Kuma a cikin littafin: "Ta shawo kan fushina," kuma a cikin littafin: "Na riga fushina."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai taba zagin abinci ba, idan ya so shi, ya ci, in kuma ya ki shi, to ya bar shi.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Saeed Al-Khudri - Allah ya yarda da shi - a cikin marfoo ': cewa wasu daga mabiya sun tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma ya ba su, sannan suka tambaye shi kuma ya ba su, har sai abin da ya mallaka ya kare, don haka ya ce da su lokacin da ya ciyar da komai a hannunsa: "Abin da nake da shi mai kyau ba zai kasance ba. Ka kiyaye shi daga gare ka, kuma duk wanda ya nemi tsari, Allah zai gafarta masa, wanda kuma ya gamsu, Allah zai wadata shi, kuma duk wanda ya yi hakuri zai yi haƙuri. Babu wanda aka ba kyauta mai kyau da fadi fiye da haƙuri.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Previous page
Page 10 of 28
Next page