Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Anas bin Malik, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Zuwa ga Allah, ina farin ciki da tuban bawansa daga dayanku. A cikin littafin: «Allah mafi yawan tuban bayinsa lokacin da ya tuba gare shi, daga ɗayanku ya kasance a kan raƙumi, ƙasar jeji, Fanflta shi da abinci da abin sha, gajiyarsu, sun zo bishiya, sun kwanta a cikin inuwa, sun yanke kauna daga raƙumi, Fbana kamar dai ita ce, jerin Tare da shi, ya ɗauki kwayayenta, sannan ya ce da farin ciki: Ya Allah, kai bawana ne, kuma ni ne Ubangijinku! Kuskure don farin ciki ".Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana Aisha da Ummu Salam Allah ya yarda da su Daga Annabi : " Asuba tana Riske shi a halin yana cikin Janaba daga Ahalinsa, Sannan yayi Wanka yayi Sallah kuma ya yi Azumi"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إذا أقبل الليل من هَهُنا، وأَدْبَرَالنهار من ههنا، فقد أفطر الصائم».متفق عليه
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa inganta) sai da niyya, kaɗai mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce".Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Sallar mutum a jama'a tana karuwa akan sallarsa agidansa a kasuwarsa da daraja ashirin da wani abu, hakan cewa dayansu idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka darajarsa da shi, an kankare masa kuskurensa da shi, har ya shiga masallaci. Idan ya shiga masallaci ya kasance a cikin sallah muddin dai sallah ce ta tsare shi , Mala'iku suna addu'a ga dayanku muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: Ya Allah ka jikansa, ya Allah ka gafarta masa, ya Allah ka karbi tubansa, muddin dai bai cutar ba a cikinsa, muddin dai bai yi (hadasi) kari ba a cikinsa ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya", Ibnu Umar ya kasance yana cewa: Idan ka kai maraice to kada ka saurari safiya, idan ka wayi gari to kada ka saurari yammaci, ka yi riƙo daga lafiyarka dan rasshin lafiyarka, kuma daga rayuwarka dan mutuwarka.Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa Musulmi, kowane Musulmi akan Musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".Bukhari ne ya rawaito shi