Hadith for the World
FIƘHU DA USULU

Fiqhun Ibada

231 hadiths

231 hadiths

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إذا أقبل الليل من هَهُنا، وأَدْبَرَالنهار من ههنا، فقد أفطر الصائم».متفق عليه
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Sallar mutum a jama'a tana karuwa akan sallarsa agidansa a kasuwarsa da daraja ashirin da wani abu, hakan cewa dayansu idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka darajarsa da shi, an kankare masa kuskurensa da shi, har ya shiga masallaci. Idan ya shiga masallaci ya kasance a cikin sallah muddin dai sallah ce ta tsare shi , Mala'iku suna addu'a ga dayanku muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: Ya Allah ka jikansa, ya Allah ka gafarta masa, ya Allah ka karbi tubansa, muddin dai bai cutar ba a cikinsa, muddin dai bai yi (hadasi) kari ba a cikinsa ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم :«عُرِضَتْ عَلَيَّ أعمالُ أُمتي، حَسَنُهَا وسَيِّئُهَا فَوَجَدتُ في مَحَاسِنِ أَعْمَالِهَا الأَذَى يُمَاطُ عَنِ الطَّرِيقِ، ووَجَدتُ في مَسَاوِئِ أَعْمَالِهَا النُّخَاعَةُ تَكُونُ في المَسْجِدِ لا تُدْفَنُ».رواه مسلم
A kan A’isha, yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta ce: Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.Muslim ne ya rawaito shi
عن عائشة رضي الله عنها والمغيرة بن شعبة رضي الله عنه : أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يقوم من الليل حتى تَتَفَطَّرَ قَدَمَاهُ فقلت له: لم تَصْنَعُ هذا يا رسول الله، وقد غفر اللهُ لك ما تقدم من ذنبك وما تأخر؟ قال: «أَفَلَا أحب أن أكونَ عبدا شَكُورًا».حديث عائشة -رضي الله عنها-: متفق عليه. حديث المغيرة بن شعبة -رضي الله عنه-: متفق عليه
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga A’isha - Allah ya yarda da ita - ta ce: “Rana ta fadi a lokacin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane addu’a. Ya tsawaita tsayi, sannan ya durkusa, ya tsawaita gwiwowi, sannan ya tashi, sannan ya kara tsayi - wanda ba shi da tsayuwa ta farko - sannan ya durkusa, sannan ya tsawaita ruku'u - wanda ba shi da ruku'u na farko - sannan ya dago da tsayi - wanda ba shi da tsayuwa ta farko - sannan ya yi sujjada, ya tsawaita sujjada, sannan ya yi a ciki Sauran rak’ah daidai yake da abin da yayi a raka’ah ta farko, sannan ya tafi, sai rana ta fito.Ya yiwa mutane huduba. Kuma suka yi sadaka. Sannan ya ce: Ya ku al'ummar Muhammadu, kuma Wallahi ba wanda ya fi Allah kishi ga bawansa na yin zina ko kuyangar sa. Ya al'ummar Muhammad, kuma da Allah, da kuna san abin da na sani, da za ku yi 'yar dariya kaɗan kuma ku yi kuka da yawa. " Kuma a cikin lafazin: "Kammala raka'a biyu da sujada huɗu."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Nana Aisha ya ce: "A kowane dare Annabi yana wutiri ko afarkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Zaid Dan Asim Almazini -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Annabi ya futo ranci Aokon ruwa, sai ya fuskanci Alkibla yana Addua, kuma ya juya kayansa baibai, kuma yayi Sallah Rakaa biyu, kuma ya bayya karatu" a wani lafazin kuma "Zuwa Wurin Sallar Idi"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullah bn Amr bn al-Aas - yardar Allah ta tabbata a gare shi - tare da isnadi: "Ku ci, ku sha, ku ba da sadaka, kuma ku sanya, ba tare da tunani ba, kuma babu almubazzaranci."Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Bukhari Ya Rawaito shi Mu'allak amma ta Sigar Yankewa - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - tare da isnadi: “Ban taba yin Sallah a bayan limami ba, ban danne wata addu’a ba, kuma ban cika wata addu’a daga Annabi mai tsira da amincin Allah ba.”Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
an karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi an daga hadisin zuwa ga Annabi: "wanda ya halarci Gawa har akai mata salla yana da kiradi guda.wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu.sai aka ce: menene kiradi biyu? sai yace: kwatankwacin manyan dutsuna biyu" a wata ruwayar kuma: "mafi kankantarsu kwatankwacin dutsen Uhudu"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Jundub bin Abdullah Al-Bajali - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi salla a ranar yanka, sa'annan ya yi huxuba, sa'annan aka yanka shi, sai ya ce: Duk wanda ya yanka kafin ya yi salla, to ya yanka wani a madadinsa, kuma wanda ba ya yanka to a yanka shi da sunan Allah".Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah, Kada ku kuskura Allah Ya kamaku da wani (laifi) cikin alƙawarinsa; domin cewa duk wanda ya nemeshi da wani abu (na laifi) Zai kamashi, sannan Ya kifar da shi ta fuskarsa a cikin wutar Jahannama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Umar bn Khattab - Allah ya yarda da shi - a cikin isnadi: “Duk wanda ya yi barci a madadin jam’iyyarsa da daddare, ko wani kan abu daga ciki, to karanta shi tsakanin sallar asuba da sallar azahar”.Muslim ne ya rawaito shi