Hadith for the World
Fiqhun Ibada

Jihadi

17 hadiths

17 hadiths

Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji...Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عبد الله بن أبي أوفى رضي الله عنه أَنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم فِي بَعْض أَيَّامه التي لَقِي فيها العدو انتظر، حتى إذا مَالَتِ الشمس قام فِيهم، فقال: «أَيُّها الناس، لا تَتَمَنَّوْا لِقَاء الْعَدُوِّ، وَاسْأَلوا الله الْعافية فَإِذا لَقِيتموهم فَاصْبِرُوا، وَاعلموا أَنَّ الْجَنَّة تحت ظِلال السُّيوف ثُمَّ قَال النَّبِي صلى الله عليه وسلم: اللهمَّ مُنزِلَ الْكتاب، وَمُجْرِيَ السَّحاب، وَهازم الأَحْزاب: اهْزِمهم، وَانصُرنا علَيهم».متفق عليه
Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshinalmiskiBukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Abi wakkas ya ce: "Munyi yaki tare da Manzon Allah Yakuna guda bakwai, muna ta cin Fara"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Zaid ɗan Khalid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bin Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah na gafarta wa shahidi komai sai addini." Kuma a cikin wata ruwaya daga gare shi cewa: “Kisa a cikin tafarkin Allah yana kankare komai face addini.”Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutumin da ya yi kuka saboda tsoron Allah ba zai shiga wuta ba har sai madara ta dawo a cikin nono, kuma babu tarin kura saboda Allah da hayakin Jahannama."Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Babu abinda Shahidi yake samunsa (Na Zafi) sai kamar abunda dayanku yake ji idan Turuwa ta cije shiAn rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu abinda Shahidi yake samunsa (Na Zafi) sai kamar abunda dayanku yake ji idan Turuwa ta cije shi"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - ya ce: Aka ce: Ya Manzon Allah, me ya kamanta jihadi saboda Allah? Ya ce: «Ba za ku iya ba», sai suka maimaita shi sau biyu ko uku, duk wannan maganar: «Ba za ku iya ba»! Sannan ya ce: "Misalin mujahid saboda Allah kamar misalin mai azumi ne wanda ya tashi tsaye yana addu'ar ayoyin Allah. Ba ya kasawa cikin azumi ko salla har sai mujahid din ya dawo ta hanyar Allah." Kuma a cikin ruwayar Bukhari: Wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ka shiryar da ni zuwa ga aikin da ke halatta jihadi? Ya ce: "Ban same shi ba." Sannan ya ce: "Shin za ku iya shiga masallacinku lokacin da mujahid ya fita ya tashi bai karya ba, kuma ya yi azumi ba ya karya azumin?" Ya ce, "Wanene zai iya yin hakan?!"Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba.Bukhari ne ya ruwaito shi, da Abu Dawud, kuma lafazin nasa ne
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Zuwa ga Annabi: "Duk wanda bai yi yaki kuma bai zantar da kansa zai yi yaki ba to zai mutu cikin Sifar Munafurci"Muslim ne ya rawaito shi
عن عمرو بن شعيب، عن أبيه، عن جده قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «يَدُ المسلمين على مَن سِواهم، تَتَكافَأُ دِماؤهم وأموالُهم، ويُجِيرُ على المسلمين أدْناهم، ويَرُدُّ على المسلمين أَقْصَاهم».رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد