Hadith for the World
FIƘHU DA USULU

Fiqhun Ibada

231 hadiths

231 hadiths

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji...Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عبد الله بن أبي أوفى رضي الله عنه أَنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم فِي بَعْض أَيَّامه التي لَقِي فيها العدو انتظر، حتى إذا مَالَتِ الشمس قام فِيهم، فقال: «أَيُّها الناس، لا تَتَمَنَّوْا لِقَاء الْعَدُوِّ، وَاسْأَلوا الله الْعافية فَإِذا لَقِيتموهم فَاصْبِرُوا، وَاعلموا أَنَّ الْجَنَّة تحت ظِلال السُّيوف ثُمَّ قَال النَّبِي صلى الله عليه وسلم: اللهمَّ مُنزِلَ الْكتاب، وَمُجْرِيَ السَّحاب، وَهازم الأَحْزاب: اهْزِمهم، وَانصُرنا علَيهم».متفق عليه
Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshinalmiskiBukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Abi wakkas ya ce: "Munyi yaki tare da Manzon Allah Yakuna guda bakwai, muna ta cin Fara"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bn Omar - Allah ya yarda da shi - "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiga Makka daga abinci, daga saman gidan yaji, ya fita daga karamar garken."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Umar - Allah ya yarda da shi -: Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Zaidu Dan Asim Almaziny -Allah ya yarda da shi- yace: ((An kai kukan Mutumin da yake jin kamar wani abu na sauti a cikinsa a lokacin salla,sai Annabi tsira da amincin Allah yace:kar ka fita daga salla har sai ka ji wata kara,ko ka ji wari)).Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).Muslim ne ya rawaito shi
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce: anyi Khusufin Rana a lokacin Manzon Allah SAW sai ya tashi a firgice, kuma yana tsoron ko tashin Al-qiyama ne. har yaje Masallaci, sai ya tashi, sai yayi sallah da mafi tsawon tsayuwa da Sujada, da ban tava ganin yayi kwatankwacinsa ba a sallarsa, sannan ya cea: "Lallai Waxan nan Ayoyi Allah ya turo su, ba wai sun kasance saboda Mutuwa wani Mutum bane ko rayuwarsa, sai dai Allah yana aiko su don ya tsorata bayinsa, to idan kuka ga wani abu daga cikin su to zabura zuwa Anbaton Allah da roqonsa da kuma neman gafararsa"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi