Hadith for the World
Fiqhun Iyali

Hukunce Hukuncen Mata

10 hadiths

10 hadiths

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta Ko ya ce: "Waninsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Shurayh Khuwailid bin Amr Al-Khuzai da Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare su - a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Ya Allah, Ina kunyatar da hakkin masu rauni: maraya da mace."Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa`id al-Khudri - yardar Allah ta tabbata a gare shi - wanda ya ce: Wata mata ta zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta ce: Ya Manzon Allah, mutanen ya tafi tare da maganarka, don haka ka sanya mana wata Rana daga gareka da za mu koya daga gareka kamar yadda ka koya daga abin da Allah ya sanar da kai Sai ya ce: kum haxu Ranar Kaza da Kaza sai suka tarun sai Manzon Allah SAW ya zo musu sai ya koyar da su abunda Allah ya sanar da shi, sannan ya ce: “Babu wata Mace daga cikinku da zata rasa 'Ya'yanta Uku sai sun kasance Mata Katanga daga Wuta" "Da biyu."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce: "Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن ابن عباس رضي الله عنهما أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لا يَخْلُوَنَّ رجلٌ بامرأةٍ، ولا تسافِرَنَّ امرأةٌ إلا ومعها محرمٌ»، فقام رجل فقال: يا رسول الله، ‌اكتتبت في غزوة كذا وكذا، وخرجت امرأتي حاجة، قال: «اذهب فحج مع امرأتك».متفق عليه