24 hadiths
Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce: "Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi