Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Daga Abu Umamah al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:

Available in 38 languages
«Daga Abu Umamah al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: «‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa, Ku karanta surori biyu Baƙara da al-Imran, domin cewa su za su zo a ranar alƙiyama kamar giza-gizai ko kamar wata tawagar tsuntsaye sun yi sahu, suna kare ma'abocinsu, ku karanta Surat al-Baƙara don haddace ta albarka ne, kuma barinta asara ne, kuma matsafa ba zasu iya ta ba».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan dawwama kan karatun Alƙur'ani; domin shi (Alkur’ani) zai yi ceto a ranar alƙiyama ga masu karanta shi masu aiki da shi, sannan ya ƙarfafa karanta surori biyu: Baƙara da al-Imran, kuma ya ambace su da Zahrawani masu haske; saboda haskensu da kuma shiryarawarsu, kuma lallai ladan karanta su da tadabburin ma'anoninsu da kuma aiki da abinda ke cikinsu, zasu zo ranar alƙiyama kamar gizagizai biyu ko wasunsu, ko ka ce su garken tsntsaye ne waɗanda suka shinfiɗa fukafukansu sashinsu na saduwa da sashi, suna yi wa ma'abocinsu inuwa kuma suna kare shi. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa dawwama a kan karanta Suratul Baƙara da tadabburin ma'anoninta da kuma aiki da abinda ke cikinsu, kuma hakan a cikinsa akwai albarka da amfani mai girma a duniya da lahira, kuma barin hakan a cikinsa akwai asara da nadama a ranar alƙiyama, kuma daga cikin falalar wannan surar matsafa ba zasu iya cutar da wanda ya karantata ba.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality