Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 44 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Mutumin da yake zagin zamani a lokacin saukar masifu da abubuwan ƙi yana cuta ta kuma yana tauyeNi; domin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai jujjuya al'amura Shi kaɗai, kuma Mai sarrafa abinda yake faruwa; to aibata zamani aibata Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, zamani kuwa kawai shi halitta ne abin horewa, abubuwa suna gudana ne a cikinsa da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality