Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bn Omar - Allah ya yarda da shi - "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiga Makka daga abinci, daga saman gidan yaji, ya fita daga karamar garken."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Umar - Allah ya yarda da shi -: Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أنس بن مالك رضي الله عنه أنَّ رَجُلاً كَانَ عِند النَبِيَّ صلى الله عليه وسلم فَمَرَّ رَجُلٌ بِهِ، فقال: يا رسول الله، أنِّي لَأُحِبُّ هَذَا، فَقَال لَهُ النَبِيُّ صلى الله عليه وسلم : «أَأَعْلَمْتَهُ؟» قال: لا. قال: «أَعْلِمْهُ»، فَلَحِقَهُ، فقال: إِنِّي أُحِبُّك فِي الله، فقال: أّحَبَّك الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.رواه أبو داود والنسائي في الكبرى وأحمد
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Abu Musa al-Ash'ari Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi: «Tsoron Allah Madaukaki: Girmama Musulmin Shaiba, kuma mai riko da Kur'ani yana da daraja a ciki, kuma ya bushe shi, da girmamawa tare da Sultan spondylitis».Abu Daud Ya Rawaito shi
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".Muslim ne ya rawaito shi
عن عمران بن حصين رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رسولُ اللَّه -صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم-: «الحَيَاءُ لاَ يَأْتِي إِلاَّ بِخَيرٍ». وفي رواية : «الحَيَاءُ خَيرٌ كُلُّهٌ» أو قال: «الحَيَاءُ كُلُّهُ خَيرٌ».الرواية الأولى: متفق عليها. الرواية الثانية والثالثة: رواها مسلم
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaice
كَانَ ابنُ عمرَ -رضِيَ الله عنهما- يَقُول لِلرَّجُل إِذَا أَرَادَ سَفَرًا: ادْنُ مِنِّي حَتَّى أُوَّدِعَكَ كَمَا كَان رسولُ الله -صلَّى الله عليه وسلَّم- يُوَدِّعُنَا، فَيقُول: «أَسْتَوْدِعُ الله دِينَكَ، وَأَمَانَتَكَ، وَخَوَاتِيمَ عَمَلِكَ». وعن عبد الله بن يزيد الخطمي رضي الله عنه- قال: كَانَ رسُول الله -صلَّى الله عليه وسلَّم- إِذَا أَرَادَ أَنْ يُوَدِّعَ الجَيشَ، قال: «أَسْتَودِعُ الله دِينَكُم، وَأَمَانَتَكُم، وخَوَاتِيمَ أَعْمَالِكُم».الحديث الأول: رواه أبو داود، والتَرمذي واللفظ له، وابن ماجه والنسائي في الكبرى وأحمد. الحديث الثاني: رواه أبو داود والنسائي الكبرى
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Zaidu Dan Asim Almaziny -Allah ya yarda da shi- yace: ((An kai kukan Mutumin da yake jin kamar wani abu na sauti a cikinsa a lokacin salla,sai Annabi tsira da amincin Allah yace:kar ka fita daga salla har sai ka ji wata kara,ko ka ji wari)).Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta Ko ya ce: "Waninsa".Muslim ne ya rawaito shi
عن شقيق بن سلمة رحمه الله قال: كان ابن مسعود رضي الله عنه يُذَكِّرُنا في كل خميس، فقال له رجل: يا أبا عبد الرحمن، لَوَدِدْتُ أنك ذَكَّرْتَنا كل يوم، فقال: أما إنه يمنعني من ذلك أني أكره أن أُمِلَّكُم، وإني أَتَخَوَّلُكُم بالمَوْعِظَةِ، كما كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَتَخَوَّلُنَا بها مَخَافَةَ السَّآمَةِ علينا.متفق عليه
Daga Abdullahi Bn Amr Bn Al-as -Allah ya yarda da su- "Baya tare da mu wabda duk baya jin tausayin Qaramin mu, kuma bai san girman Babbanmu ba"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
عن يزيد بن حيان قال: انطلقت أنا وحُصين بن سَبْرَة وعمرو بن مسلم إلى زيد بن أرقم رضي الله عنه فلما جلسنا إليه قال له حصين: لقد لقيتَ يا زيد خيرًا كثيرًا، رأيتَ رسول الله صلى الله عليه وسلم وسمعتَ حديثه، وغزوتَ معه، وصليتَ خلفه: لقد لقيت يا زيد خيرًا كثيرًا، حدثنا يا زيد ما سمعت من رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: يا ابن أخي، والله لقد كَبِرَتْ سني، وقَدُمَ عهدي، ونسيتُ بعض الذي كنت أَعِي من رسول الله صلى الله عليه وسلم فما حدثتكم فاقبلوا، وما لا فلا تُكَلِّفُونِيهِ. ثم قال: قام رسول الله صلى الله عليه وسلم يومًا فينا خطيبًا بماء يُدعى خُمًّا بين مكة والمدينة، فحمد الله، وأثنى عليه، ووعظ وذكَّر، ثم قال: «أما بعد، ألا أيها الناس، فإنما أنا بشر يُوشِكُ أن يأتي رسول ربي فأُجِيبَ، وأنا تاركٌ فيكم ثَقَلَيْنِ: أولهما كتاب الله، فيه الهدى والنور، فخذوا بكتاب الله، واستمسكوا به»، فحَثَّ على كتاب الله، ورغَّبَ فيه، ثم قال: «وأهل بيتي أُذَكِّرُكُمُ اللهَ في أهل بيتي، أُذَكِّرُكُمُ اللهَ في أهل بيتي» فقال له حصين: ومن أهل بيته يا زيد، أليس نساؤه من أهل بيته؟ قال: نساؤه من أهل بيته، ولكن أهل بيته من حُرِمَ الصدقةَ بعده، قال: ومن هم؟ قال: هم آل علي، وآل عقيل، وآل جعفر، وآل عباس. قال: كل هؤلاء حُرِمَ الصدقةَ؟ قال: نعم. وفي رواية: «ألا وإني تاركٌ فيكم ثَقَلَيْنِ: أحدهما كتاب الله وهو حبل الله، من اتبعه كان على الهدى، ومن تركه كان على ضلالة».رواه مسلم
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi