Hadith for the World
Fiqihun Halaye

Kyawawan Halaye

35 hadiths

35 hadiths

Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce: Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عَن أَبي هُرَيْرَةَ، قَالَ: قَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي صَلاَةٍ وَقُمْنَا مَعَهُ، فَقَالَ أَعْرَابِيٌّ وَهُوَ فِي الصَّلاَةِ: اللَّهُمَّ ارْحَمْنِي وَمُحَمَّدًا، وَلاَ تَرْحَمْ مَعَنَا أَحَدًا. فَلَمَّا سَلَّمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لِلْأَعْرَابِيِّ: «لَقَدْ حَجَّرْتَ وَاسِعًا» يُرِيدُ رَحْمَةَ اللهِ.رواه البخاري
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ اللَّهَ قَالَ: إِذَا ابْتَلَيْتُ عَبْدِي بِحَبِيبَتَيْهِ فَصَبَرَ، عَوَّضْتُهُ مِنْهُمَا الجَنَّةَ» يُرِيدُ: عَيْنَيْهِ.رواه البخاري