Hadith for the World
ILIMIN AƘIDA

Sunaye da Hukunce Hukunce

22 hadiths

22 hadiths

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi zuwa ga Manzon Allah: "Imani kashi sba;in da Tara ne ko kuma kashi Sittin da Tara, mafificinsu shi ne faxin babu wani abun bauta da gaskiya sai Allah, Mafi qanqanta kuma shi ne gusar da cuta ga barin Hanya, kuma kunya wani yanki ne daga cikin Imani"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".Ahmad ne ya rawaito shi
Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai baAhmad ne ya rawaito shi
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".Muslim ne ya rawaito shi
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "ثَلاَثٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ وَجَدَ حَلاَوَةَ الإِيمَانِ: أَنْ يَكُونَ اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَحَبَّ إِلَيْهِ مِمَّا سِوَاهُمَا، وَأَنْ يُحِبَّ المَرْءَ لاَ يُحِبُّهُ إِلَّا لِلَّهِ، وَأَنْ يَكْرَهَ أَنْ يَعُودَ فِي الكُفْرِ كَمَا يَكْرَهُ أَنْ يُقْذَفَ فِي النَّارِ".متفق عليه
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".Muslim ne ya rawaito shi
عن جابر بن عبد الله قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا خطب احمرَّتْ عيناه، وعلا صوته، واشتد غضبه، حتى كأنه مُنذِرُ جيشٍ يقول: صبَّحكم ومسَّاكم، ويقول: «بُعثتُ أنا والساعةُ كهاتين»، ويقرن بين إصبعيه السبابة، والوسطى، ويقول: «أما بعد، فإن خير الحديث كتاب الله، وخير الهدى هدى محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل بدعة ضلالة» ثم يقول: «أنا أولى بكل مؤمن من نفسه، من ترك مالًا فلأهله، ومن ترك دينًا أو ضَياعًا فإليَّ وعليَّ».رواه مسلم