FIƘHU DA USULU
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Available in 53 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".»Meaning translation ·
Saved at original quality








