Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullah bn Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Daya daga cikin manyan zunubai shi ne mutum ya zagi iyayensa." Aka ce: Shin mutumin yana zagin iyayensa ne? Sai ya ce: Ee, ya zagi mahaifin mutum, ya zagi mahaifinsa, mahaifiyarsa kuma ta zagi mahaifiyarsa.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - tare da isnadi: “Ban taba yin Sallah a bayan limami ba, ban danne wata addu’a ba, kuma ban cika wata addu’a daga Annabi mai tsira da amincin Allah ba.”Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"Muslim ne ya rawaito shi
an karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi an daga hadisin zuwa ga Annabi: "wanda ya halarci Gawa har akai mata salla yana da kiradi guda.wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu.sai aka ce: menene kiradi biyu? sai yace: kwatankwacin manyan dutsuna biyu" a wata ruwayar kuma: "mafi kankantarsu kwatankwacin dutsen Uhudu"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Jundub bin Abdullah Al-Bajali - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi salla a ranar yanka, sa'annan ya yi huxuba, sa'annan aka yanka shi, sai ya ce: Duk wanda ya yanka kafin ya yi salla, to ya yanka wani a madadinsa, kuma wanda ba ya yanka to a yanka shi da sunan Allah".Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
A kan Abu Dhar al-Ghafari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: “Shin ba zan gaya muku abin da nake son fada wa Allah ba? Mafi soyuwa ga magana ga Allah: Tsarki ya tabbata ga Allah da yabo.Muslim ne ya rawaito shi
A kan Uday bin Umayrah al-Kindi - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: “Duk wanda ya yi amfani da shi a cikin aiki, kuma muka ɓoye sutura da abin da ke sama da shi, zai zama mai saro wanda zai zo da shi ranar tashin kiyama.” Don haka sai wani bakar fata daga Ansar ya tashi zuwa gare shi, kamar ina kallonsa, sai ya ce: Ya Manzon Allah, karbi aikinka daga wurina. Ya ce: Na ji kuna cewa irin wannan da irin wannan, sai ya ce: "Yanzu nake fada: Duk wanda muka yi amfani da shi na aiki, to ya shigo da kadan da yawa. Abin da aka ba shi ya karba, kuma abin da aka haramta daga gare shi ya kare."Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah, Kada ku kuskura Allah Ya kamaku da wani (laifi) cikin alƙawarinsa; domin cewa duk wanda ya nemeshi da wani abu (na laifi) Zai kamashi, sannan Ya kifar da shi ta fuskarsa a cikin wutar Jahannama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jariri ɗan Abbdullah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Umar bn Khattab - Allah ya yarda da shi - a cikin isnadi: “Duk wanda ya yi barci a madadin jam’iyyarsa da daddare, ko wani kan abu daga ciki, to karanta shi tsakanin sallar asuba da sallar azahar”.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci".Bukhari ne ya rawaito shi
A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da tashe: "Da wanda raina yake a hannunsa, da ba ku yi zunubi ba, da Allah zai fita daga gare ku, kuma ya zo da mutanen da suka yi zunubi, kuma suna neman gafara daga Allah Madaukaki, kuma zai gafarta musu."Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Jabir Bn Abdullah -Allah ya yarda da su- "Kowane bawa za a tayar da shi ranar tashin kiyama a cikin yanayin da ya mutu. a kansa"Muslim ne ya rawaito shi