Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Abdullah bn Masoud - Allah ya yarda da shi - tare da rahoto: "Za a shigar da Jahannama a wannan rana a kansa saboda iyayengiji dubu saba'in, tare da kowace sarauta ta sarakuna dubu saba'in da suke jan ta."Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makoma ta take, Ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri’’.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar. "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad
Daga Abdullahi bn Omar - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Mumini wanda yake cudanya da mutane kuma ya yi hakuri da cutarwarsu ya fi wanda ba ya cakuduwa da mutane kuma ya yi hakuri da cutarwarsu".Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Mumini madubin dan uwansa mumini ne".Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa: «‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai". ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne. Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce: "Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi