Hadith for the World
Topic

FALALOLI DA LADUBBA

288 hadiths

288 hadiths

An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- "cewa shi ya wuce Yara sai yayi musu sallama, ya ce Annabi ya kasance yanayin hakanBukhari da Muslim suka Rawaito shi
An rawaito daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi -daga Annabi: "Duk wanda aka bashi Raihan, to kada yaki karba, saboda yana saukin dauka, ga kuma dadin Kamshi"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce: Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ubaidullahi ɗan Mihsan al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».Tirmizi ne ya Rawaito shi
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Zaid Dan Arƙam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ba zan faɗa muku (komai ba) sai kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana faɗa: Ya kasance yana cewa: «‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da zuciyar da bata risina, da zuciyar da ba ta ƙoshi, da addu'ar da ba'a amsarta ».Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya Kasance idan zai tafi zuwa Makwancinsa yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inci"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inciBukhari da Muslim suka Rawaito shi
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya Manzon Allah yana cewa: "Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga gajiyawa, da Kasala, da Tsoro, da Tsufa, da Rowa, kuma ina neman tsarinka daga Azabar Kabari, Kuma ina neman tsarinka daga fitinar Rayuwa da ta Mutuwa" a kuma cikin wata riwayar kuma: "Kuma ..............Bashi da Galabar Mutane"Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni: "ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiyaMuslim ne ya rawaito shi
Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.Muslim ne ya rawaito shi
An karbo daga Anas Allah Ya yarda da shi, ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «إذا أوى أحدكم إلى فراشه فَليَنْفُضْ فِرَاشَهُ بِدَاخِلَةِ إزَارِهِ فإنَّهُ لا يدري ما خلفه عليه، ثم يقول: باسمك ربي وضعت جنبي، وبك أرفعه، إن أمسكت نفسي فارحمها، وإن أرسلتها، فاحفظها بما تحفظ به عبادك الصالحين».متفق عليه
Da Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya" kuma cikin wata Riwayar Sufyan Al-Sauri ya ce: Ina kokwanton ni na kara daya daga cikin su.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi