Hadith for the World
Topic

FALALOLI DA LADUBBA

288 hadiths

288 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makoma ta take, Ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri’’.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar. "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Mumini madubin dan uwansa mumini ne".Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa: «‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai". ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne. Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce: "Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce: "Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"Buhari ne ya rawaito shi
Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Sauban -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Lallai Musulmi idan ya gaida Dan Uwansa Musulmi yana cikin fukakukan Al-jannah har sai ya dawo, aka ce ya manzon Allah Me nene Khurfar Al-jannah? ya ce: Fukafukanta"Muslim ne ya rawaito shi
عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه كان إذا أكل طعاما، لعق أصابعه الثلاث. قال: وقال: «إذا سقطت لُقمة أحدكم فليُمِطْ عنها الأذى، وليأكلها ولا يَدَعْهَا للشيطان» وأمر أن تُسْلَتَ القَصْعَةُ، قال: «فإنكم لا تدرون في أيِّ طعامكم البركة» وعن جابر بن عبد الله رضي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قالَ: "إنّ الشيطانَ يَحضُرُ أحدَكُم عندَ كلِ شيءٍ من شَأنِه، حتى يَحضُرَهُ عندَ طعامِهِ، فإذا سَقطتْ لقمةُ أحدِكُم فليَأخُذْها فَلْيُمِطْ ما كانِ بها من أذى، ثم ليَأكُلْها ولا يَدَعْها للشيطانِ، فإذا فَرَغَ فليَلْعَقْ أصابعَهُ، فإنه لا يَدري في أيِّ طَعامه البركة"حديث أنس رواه مسلم. حديث جابر رواه مسلم
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi