Hadith for the World
FIƘHU DA USULU

Fiqhun Ibada

231 hadiths

231 hadiths

Daga Uƙuba ɗan Amir al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu: Lokacin da rana ta fito a bayyane har sai ta ɗaga, da kuma lokacin da ta tsaya a tsakiyar sama har sai ranar ta karkace, da kuma lokacin da ranar ta kusa faɗuwa har sai ta faɗi.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jubair Bn Mux'im -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Cewa Manzon ALlah SAW ya hana Sallah a tsakiyar Rana har sai Rana ta karya sai dai Ranar Jumu'a"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Bn Al-Shakhir -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Naga Manzon Allah SAW yana Sallah a cikin qirjinsa da wani Ruri Kamar Rurin Dutsen Niqa saboda Kuka SAW"Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Anas bin Malik - Allah ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan za a kawo abincin dare, fara da shi kafin ku yi sallar Magriba, kuma kada ku yi sauri da cin abincinku.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - cewa Annabi -SAW- ya ga Kaki a Al-kibla, don haka yana da wahala gare shi har sai da aka ganshi a fuskarsa, don haka sai ya tashi ya goge da hannunsa. Tsakaninsa da Kibla, ba ɗayanku ya tofa albarkacin bakinsa, sai a hagu ko a ƙasan ƙafafunsa. ”Sa’annan ya ɗauki ƙarshen tufafinsa, ya tofa a ciknsa, sa’annan wasunku suka amsa, suka ce:“ Ko ya aikata hakan. ”Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce Manzon Allah ya buxe mana labule kuma Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar sai ya ce: "Ya ku Mutane babu abunda ya ragu daga cikin Alamomin Annabta sai Kyakkyawan Mafarkin da Musulmi zai ganshi, ko a ganar masa, ku saurara kuma lallai ni ina hana karanta Al-qur'ani a a Ruku'u ko a Sujada amma a Ruku'u ku girmama Allah kuma a Sujada to kuyi qoqrin Addu'a an kusa a amsa Muku"Muslim ne ya rawaito shi
عن الحكم قال: غَلَب على الكُوفة رجُل -قد سَمَّاه- زَمَنَ ابن الأشْعَث، فأمر أبَا عُبيدة بن عبد الله أن يصلِّي بالناس، فكان يصلِّي، فإذا رَفع رأسه من الرُّكوع قام قَدْر ما أقُول: اللَّهُم ربَّنا لك الحَمد، مِلْءَ السَّماوات ومِلْءَ الأرض، ومِلْءَ ما شِئت من شَيء بعد، أهْل الثَّناء والمَجد، لا مانع لما أعْطَيت، ولا مُعْطِي لما مَنعت، ولا يَنفع ذَا الجَدِّ مِنْك الجَدِّ. قال الحَكم: فَذَكَرت ذلك لعَبد الرَّحمن بن أبي ليلى فقال: سمعت البَرَاء بن عَازب يقول: «كانت صلاة رسول الله صلى الله عليه وسلم وركُوعه، وإذا رفع رأسه من الرُّكوع، وسُجوده، وما بَيْن السَّجدتين، قريبًا من السَّوَاء» قال شُعبة: فذَكَرْتُه لِعَمرو بن مُرَّة فقال: قد رأيت ابن أبي ليلى، فلم تَكن صلاته هكذا.رواه مسلم
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- Lallai cewa Manzon Allah SAW ya kasance baya Al-qunuti sai in zai Addu'a ga wasu Mutane, ko yayi Addu'a kan wasu MutaneIbn Khuzaimah ya rawaito shi
Daga Sauban, Allah Ya yarda da shi: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce: Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne: Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".Nasa'i ne ya rawaito shi a cikin Al-Kubra
Daga Imaran Ɗan Husain Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na kasance Ina da basir, sai na tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da sallah sai ya ce: Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki.Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba shin uku ne ko huɗu, to ya watsar da kokwanton, ya yi gini akan abinda ya yi yaƙini, sannan ya yi sujjada, sujjada biyu kafin ya yi sallama, idan ya kasance ya sallaci raka'a biyar za su yi masa shafa'in sallarsa, idan ya kasance ya yi sallar dan cika huɗun to sun zama turbuɗe hancin Shaiɗan".Muslim ne ya rawaito shi
عن أبي رافع أن أبا هريرة رضي الله عنه قرأ لهم: «إذا السماء انْشَقَّتْ» فسجد فيها، فلما انصَرَفَ أخبرهم أن رسول الله صلى الله عليه وسلم سجد فيها.متفق عليه
عن أبي بكرة، عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه كان «إذا جاءه أمرُ سرورٍ، أو بُشِّرَ به خَرَّ ساجدًا شاكرًا لله».رواه أبو داود وابن ماجه والترمذي وأحمد
عن حفصة رضي الله عنها «أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يُصلي ركعتين خَفيفتين بعد ما يَطلع الفجر»، وفي رواية: قبل أن تُقام الصلاة.رواه البخاري
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).Bukhari ne ya rawaito shi