Hadith for the World
FALALOLI DA LADUBBA

Falaloli

64 hadiths

64 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"Muslim ne ya rawaito shi
A kan Abu Dhar al-Ghafari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: “Shin ba zan gaya muku abin da nake son fada wa Allah ba? Mafi soyuwa ga magana ga Allah: Tsarki ya tabbata ga Allah da yabo.Muslim ne ya rawaito shi
A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da tashe: "Da wanda raina yake a hannunsa, da ba ku yi zunubi ba, da Allah zai fita daga gare ku, kuma ya zo da mutanen da suka yi zunubi, kuma suna neman gafara daga Allah Madaukaki, kuma zai gafarta musu."Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce: "Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
عن علي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقول: « مَا مِنْ مُسْلِم يَعُودُ مُسْلِماً غُدْوة إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُمْسِي، وَإنْ عَادَهُ عَشِيَّةً إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُصْبحَ، وَكَانَ لَهُ خَرِيفٌ في الْجَنَّةِ».رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane Kamar Ma'adanan Zinare da Azurfa ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kuma Rayuka Kamar Rundunar yaki ce, duk wanda suka San juna sai su Saba, wanda kuma suka saba kuma sai suki jituwa" kuma an rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah ya ce: "Zaku samu Mutane Kamar ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kumazaku samu zababbu a cikin Mutane a wannan Al-amari su ne Mafiya tsananin kinsa, kuma zaku samu Mafi Sharrin Mutane Masu fuska biyu, wanda zai zowa wadan nan da wata fuska kuma wadan nan da wata Fuskar daban"Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai SassarfaBuhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Huraira =Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah: "Allah Maxauakai yana cewa idan bawa na ya so yin savo, kada ku rubuta shi har sai ya aikata, idan kuma ya aikata shi to ku rubuta masa kwatankwacinsa, kuma idan ya barshi saboda ni to ku rubuta masa lada, kuma idan yai nufin yin aikin lada sai naiyi ba to ku rubuta masa ladan aiki xaya, idan kuma ya aika shi to ku rubuta masa lada goma har zuwa ninki xari bakwai"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «من قتل وَزَغَةً فِي أَوَّلِ ضَرْبَةٍ فله كذا وكذا حسنة، ومن قتلها في الضَّرْبَةِ الثانية فله كذا وكذا حسنة دون الأولى، وإن قتلها في الضربة الثالثة فله كذا وكذا حسنة». وفي رواية: «من قتل وَزَغًا في أول ضربة كتب له مائة حسنة، وفي الثانية دون ذلك، وفي الثالثة دون ذلك».رواه مسلم
Daga Abu Sa`id al-Khudri - yardar Allah ta tabbata a gare shi - wanda ya ce: Wata mata ta zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta ce: Ya Manzon Allah, mutanen ya tafi tare da maganarka, don haka ka sanya mana wata Rana daga gareka da za mu koya daga gareka kamar yadda ka koya daga abin da Allah ya sanar da kai Sai ya ce: kum haxu Ranar Kaza da Kaza sai suka tarun sai Manzon Allah SAW ya zo musu sai ya koyar da su abunda Allah ya sanar da shi, sannan ya ce: “Babu wata Mace daga cikinku da zata rasa 'Ya'yanta Uku sai sun kasance Mata Katanga daga Wuta" "Da biyu."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Dharr - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: An gaya wa Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - Shin kun ga wani mutum da ya aikata aiki na gari, sai mutane suka yabe shi? Ya ce: "Wannan bishara ce ta mumini."Muslim ne ya rawaito shi