Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».Bukhari ne ya rawaito shi
An rawaito daga Amr Bn Al-As -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya ce:"Ka Sadar da Azumin mu da azumin Ahlulkitab cin Sahur"Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Talha Bn Ubaidillah -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi -"Bawa ba zai taba kaiwa Matakin Masu tsoron Allaba har sai ya bar abunda babu laifi a cikinsa, da kuma zaman lafiya da Musulunci, Ubangijinka Allah, Jaririn watan Shiriya da kuma Alkairi"Ibnu Abi Hatim ya rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi
عن البراء بن عازب –رضي الله عنهما- قال: كانَ رجلٌ يَقرَأُ سُورةَ الكهفِ، وعندَه فَرَسٌ مَربُوطٌ بِشَطَنَيْنِ، فَتَغَشَّتْهُ سَحَابَةٌ فَجَعَلَتْ تَدْنُو، وجَعلَ فَرَسُه يَنفِرُ منها، فلمّا أصبحَ أتَى النبيَّ صلى الله عليه وسلم فَذَكرَ ذلك له، فقالَ: «تِلكَ السَّكِينةُ تَنَزَّلَتْ للقُرآنِ».متفق عليه
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi, ya kasance yana haɗuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadan sai su yi nazaran shi AlƘu'ani, to Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta ta alheri daga iskar da aka aiko.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi-ya ce:Manzon Allah ya kasance yana bude baki da danyan dabino kafin yayi salla, idan babu danyan dabino sai yayi da bushasshen Dabino, idan babu sai ya kurbi wani abu daga Ruwa"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
عن جابر رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا إِذَا صَعِدْنَا كَبَّرْنَا، وَإِذَا نَزَلْنَا سَبَّحْنَا. عن ابن عمر رضي الله عنهما قالَ: كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم وجيُوشُهُ إِذَا عَلَوا الثَّنَايَا كَبَّرُوا، وَإِذَا هَبَطُوا سَبَّحُوا.حديث جابر -رضي الله عنه- رواه البخاري. حديث ابن عمر -رضي الله عنهما- رواه أبو داود
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".Muslim ne ya rawaito shi
عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم ، قَالَ: «لا يدخلُ الجنةَ مَن كان في قلبه مِثقال ذرةٍ من كِبر» فقال رجل: إنّ الرجلَ يحب أن يكون ثوبه حسنا، ونَعله حسنة؟ قال: «إنّ الله جميلٌ يحب الجمالَ، الكِبر: بَطَرُ الحق وغَمْطُ الناس».رواه مسلم
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.Muslim ne ya rawaito shi
عن عائشة رضي الله عنها قالت: لم يكن النبي صلى الله عليه وسلم يصوم مِنْ شهر أكثر من شعبان، فإنّه كان يصوم شعبان كله. وفي رواية: كان يصوم شعبان إلا قليلا.متفق عليه
Daga Abu Zauhair ɗan Ru'aibatu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba".Muslim ne ya rawaito shi
عن عبدالله بن عباس رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَئِن بَقِيتُ إلى قابلٍ لأصومنّ التاسِع».رواه مسلم
Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.Bukhari ne ya rawaito shi
عن أنس رضي الله عنه ، قَالَ: مَا مَسِسْتُ دِيبَاجاً وَلاَ حَرِيراً ألْيَنَ مِنْ كَفِّ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم ، وَلاَ شَمَمْتُ رَائِحَةً قَطُّ أطْيَبَ مِنْ رَائِحَةِ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم ، وَلَقَدْ خدمتُ رسول اللهِ صلى الله عليه وسلم عَشْرَ سنين، فما قَالَ لي قَطُّ: أُفٍّ، وَلاَ قَالَ لِشَيءٍ فَعَلْتُهُ: لِمَ فَعَلْتَه؟، وَلاَ لشَيءٍ لَمْ أفعله: ألاَ فَعَلْتَ كَذا؟.متفق عليه. تنبيه: أخرجه البخاري ومسلم في حديثسن متفرقين في موضعين
Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba.Bukhari ne ya ruwaito shi, da Abu Dawud, kuma lafazin nasa ne
عن علي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقول: « مَا مِنْ مُسْلِم يَعُودُ مُسْلِماً غُدْوة إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُمْسِي، وَإنْ عَادَهُ عَشِيَّةً إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُصْبحَ، وَكَانَ لَهُ خَرِيفٌ في الْجَنَّةِ».رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne, kuma kwatankwacin munafikin da yake karanta AlKurani kamar nana ne kanshinsa mai dadi ne amma dandanonta mai daci ne, kuma kwatankawacin munafikin da ba ya karanta AlKura'ni kwatankwacin guna ce ba ta da kanshi, kuma dandanonta mai daci ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce: Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci.Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".Muslim ne ya rawaito shi