Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

عن زيد بن خالد الجهني رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: «مَنْ فَطَّرَ صائمًا، كان له مِثْلُ أجْرِهِ، غَيْرَ أنَّهُ لاَ يُنْقَصُ مِنْ أجْرِ الصَّائِمِ شَيْءٌ».رواه الترمذي وابن ماجه والنسائي في الكبرى والدارمي وأحمد
Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so" sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ya Allah Ya mai jujjuya zukata Ka juya zukatanmu a kan biyayyarKa".Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane Kamar Ma'adanan Zinare da Azurfa ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kuma Rayuka Kamar Rundunar yaki ce, duk wanda suka San juna sai su Saba, wanda kuma suka saba kuma sai suki jituwa" kuma an rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah ya ce: "Zaku samu Mutane Kamar ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kumazaku samu zababbu a cikin Mutane a wannan Al-amari su ne Mafiya tsananin kinsa, kuma zaku samu Mafi Sharrin Mutane Masu fuska biyu, wanda zai zowa wadan nan da wata fuska kuma wadan nan da wata Fuskar daban"Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa
Yana kan mutum musulmi ji da kuma da’a a cikin abin da yake so ko yake ki sai dai in an umarce shi da sabo, to idan an umarce shi da sabo to babu ji kuma babu da’a, kuma ya ce kadai ana da’a ne a cikin abin da shari ta san da shiBukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce: Ba'a taɓa ba wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zabi ba tsakanin abubuwa biyu face sai ya zaɓi mafi sauƙinsu, matuƙar bai kasance saɓo ba, idan ya kasance saɓo ne to ya kasance ya fi kowa nisantar shi, kuma Annabi bai bai taɓa ramuwar gayya ga kansa ba ko sau ɗaya, sai dai idan an keta hurumin Allah, sai ya yi hukunci saboda Allah da ita.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Zuwa ga Annabi: "Duk wanda bai yi yaki kuma bai zantar da kansa zai yi yaki ba to zai mutu cikin Sifar Munafurci"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshiBukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai SassarfaBuhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abdullahi Bn Akim -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Tarik Ɗan Ashyam al’Ashja’i, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi yana cewa: Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din sa
Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Bai Kamata Musulmi ya zamanto mai yawan tsinuwa ba"Muslim ne ya rawaito shi
عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «مَنْ أحَبَّ لِقَاءَ اللهِ أَحَبَّ اللهُ لِقَاءهُ، وَمَنْ كَرِهَ لِقَاءَ اللهِ كَرِهَ اللهُ لِقَاءهُ» فقلتُ: يا رسولَ اللهِ، أكَراهِيَةُ المَوتِ، فَكُلُّنَا نَكْرَهُ المَوتَ؟ قال: «لَيْسَ كَذَلِكَ، ولكِنَّ المُؤْمِنَ إذَا بُشِّرَ بِرَحْمَةِ اللهِ وَرِضْوَانِهِ وَجَنَّتِهِ أَحَبَّ لِقَاءَ اللهِ فَأَحَبَّ اللهُ لِقَاءهُ، وإنَّ الكَافِرَ إذَا بُشِّرَ بِعَذابِ اللهِ وَسَخَطهِ كَرِهَ لِقَاءَ اللهِ وكَرِهَ اللهُ لِقَاءهُ».رواه مسلم، ورواه البخاري عن عائشة -رضي الله عنها- في ضمنه حديث عن عبادة بن الصامت-رضي الله عنه-. رواه عن أبي موسى -رضي الله عنه- مختصرا