Hadith for the World
Topic

FIƘHU DA USULU

288 hadiths

288 hadiths

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya nemi wani wanda yake bin sa bashi, sai ya ɓuya daga gare shi, sai ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, sai ya ce: (tskaninka da) Allah? ya ce: (tsakanina da) Allah? ya ce: Lallai ni naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Salem bn Abdullah bn Omar bn Al-Khattab - Allah ya yarda da su - a kan babansa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutumin ya yi albarka, Abdullahi, idan yana cikin dare yana sallah." Salem ya ce: Abdullahi ba zai yi barci ba bayan wannan Kadan a dare.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Nana Aisha da Ummu Salam Allah ya yarda da su Daga Annabi : " Asuba tana Riske shi a halin yana cikin Janaba daga Ahalinsa, Sannan yayi Wanka yayi Sallah kuma ya yi Azumi"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إذا أقبل الليل من هَهُنا، وأَدْبَرَالنهار من ههنا، فقد أفطر الصائم».متفق عليه
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce".Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Sallar mutum a jama'a tana karuwa akan sallarsa agidansa a kasuwarsa da daraja ashirin da wani abu, hakan cewa dayansu idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka darajarsa da shi, an kankare masa kuskurensa da shi, har ya shiga masallaci. Idan ya shiga masallaci ya kasance a cikin sallah muddin dai sallah ce ta tsare shi , Mala'iku suna addu'a ga dayanku muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: Ya Allah ka jikansa, ya Allah ka gafarta masa, ya Allah ka karbi tubansa, muddin dai bai cutar ba a cikinsa, muddin dai bai yi (hadasi) kari ba a cikinsa ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم :«عُرِضَتْ عَلَيَّ أعمالُ أُمتي، حَسَنُهَا وسَيِّئُهَا فَوَجَدتُ في مَحَاسِنِ أَعْمَالِهَا الأَذَى يُمَاطُ عَنِ الطَّرِيقِ، ووَجَدتُ في مَسَاوِئِ أَعْمَالِهَا النُّخَاعَةُ تَكُونُ في المَسْجِدِ لا تُدْفَنُ».رواه مسلم