Hadith for the World

All hadiths

The complete card collection, filter by chapter

655 hadiths

Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi
Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: "An aiko manzon Allah SAW yana Xan Shekara Arba'in, kuma ya zauna a Makka Shekara goma sha Uku ana yi masa Wahayi, Sannan aka umarce shi da yayi Hijira sai yayi Hijira Shekara goma, kuma ya Mutu yana Xan Shekara Sittin da Uku"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Al-Miswar bn makhrama- Allah ya yarda da su- Zuwa ga Annabi: "Faxima wata tsokace daga gare ni, duk wanda ya vata mata to ya vata mun"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Duk wanda Ya so Hassan da Husaini to haqiqa ya so ni, kuma duk wanda yaqi su to haqiqa ya qini"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Mafificinku shi ne mafoficinku ga Ahalina baya na, ya ce sai Abdul-rahman Bn Auf ya sayar da Gona da Dubu Dari, sai ya rabata ga Matan Annabi SAW"Ibnu Abi Asim ya rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi
An Rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yardav da ita, ta ce: "Ban taba yin kishi da wata Mata daga cikin Matan Annabi SAW sai akan Khadija, kuma ni ban risketa ba, ta ce: Kuma Manzon Allah ya Kasance idan ya yanka Akuya, sai ya ce: ku aika da ita zuwa kawayen Khadija" sai ta ce sai na bashi haushi wata rana sai na ce: Khadija, sai Manzon Allah SAW ya ce: "lallai ni Allah ya Azurtani da sonta"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi bai Aure kan Khadija ba har saida ta Mutu"Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- "Lallai Cewa Mala'ika Jibril ya o da Hoton Nana Aisha a cikin wani koren kyalle na Alhari ni sai ya ce: wannan ce Matarka ce a Duniya da Lahira"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi
An karvo daga Abu Musa -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar fir'auna, da Maryam Bint Imran, kuma lallai cewa Falalar Aisha akan sauran Mata kamar Falalar Al-tharid kan sauran abinci"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdulrahman Bin Abi Umairah kuma ya kasance daga cikin sahabban Manzon Allah SAW daga Annabi SAW cewa shi ya ce da Mu'awiya: "Ya Ubangiji kasanya shi Shiyayye kuma maishiryarwa kuma ka shiryar da shi"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
An karvo daga Abi Izza Al-huzali -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Al-Tayalisi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice, idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna ne to yana daga cikin 'yan aljanna, idan ya kasance daga cikin 'yan wuta to yana daga cikin 'yan wuta, sai a ce: Wannan mazauninka ne har sai Allah Ya tasheka ranar alƙiyama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أسامة بن زيد رضي الله عنهما قال: أشرفَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم على أُطُم من آطام المدينة، فقال: «هل ترون ما أرى؟» قالوا: لا، قال: «فإنِّي لأرى الفتنَ تقع خِلال بيوتكم كوَقْع القَطْر».متفق عليه
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba shin uku ne ko huɗu, to ya watsar da kokwanton, ya yi gini akan abinda ya yi yaƙini, sannan ya yi sujjada, sujjada biyu kafin ya yi sallama, idan ya kasance ya sallaci raka'a biyar za su yi masa shafa'in sallarsa, idan ya kasance ya yi sallar dan cika huɗun to sun zama turbuɗe hancin Shaiɗan".Muslim ne ya rawaito shi
عن أبي رافع أن أبا هريرة رضي الله عنه قرأ لهم: «إذا السماء انْشَقَّتْ» فسجد فيها، فلما انصَرَفَ أخبرهم أن رسول الله صلى الله عليه وسلم سجد فيها.متفق عليه
عن أبي بكرة، عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه كان «إذا جاءه أمرُ سرورٍ، أو بُشِّرَ به خَرَّ ساجدًا شاكرًا لله».رواه أبو داود وابن ماجه والترمذي وأحمد
عن حفصة رضي الله عنها «أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يُصلي ركعتين خَفيفتين بعد ما يَطلع الفجر»، وفي رواية: قبل أن تُقام الصلاة.رواه البخاري
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Ummu Habiba - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
عن عبدالله بن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «رحم الله امرأ صلى قبل العصر أربعًا».رواه أبو داود والترمذي وأحمد
عن عبد الله بنِ مُغَفَّلِ المُزَنِيِّ رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «صَلُّوا قبل المغرب ركعتين»، ثم قال: «صَلُّوا قبل المغرب ركعتين لمن شاء»، خشية أن يتخذها الناس سُنة.رواه البخاري
عن عائشة رضي الله عنها قالت: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا سَكَتَ المؤذن بالأولى من صلاة الفجر قام، فركع ركعتين خفيفتين قبل صلاة الفجر، بعد أن يَسْتَبينَ الفجر، ثم اضطجع على شِقِّهِ الأيمن، حتى يأتيه المؤذن للإقامة».متفق عليه
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi