Hadith for the World
Topic

ILIMIN AƘIDA

135 hadiths

135 hadiths

Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Lokacin da Allah ya halicci halitta, ya rubuta a cikin wani littafi, kuma yana tare da shi a kan karaga: Rahamata ta rinjayi fushina." Kuma a cikin littafin: "Ta shawo kan fushina," kuma a cikin littafin: "Na riga fushina."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Jabir Bn Abdullah -Allah ya yarda da su- "Kowane bawa za a tayar da shi ranar tashin kiyama a cikin yanayin da ya mutu. a kansa"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".Muslim ne ya rawaito shi
عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه كان إذا أكل طعاما، لعق أصابعه الثلاث. قال: وقال: «إذا سقطت لُقمة أحدكم فليُمِطْ عنها الأذى، وليأكلها ولا يَدَعْهَا للشيطان» وأمر أن تُسْلَتَ القَصْعَةُ، قال: «فإنكم لا تدرون في أيِّ طعامكم البركة» وعن جابر بن عبد الله رضي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قالَ: "إنّ الشيطانَ يَحضُرُ أحدَكُم عندَ كلِ شيءٍ من شَأنِه، حتى يَحضُرَهُ عندَ طعامِهِ، فإذا سَقطتْ لقمةُ أحدِكُم فليَأخُذْها فَلْيُمِطْ ما كانِ بها من أذى، ثم ليَأكُلْها ولا يَدَعْها للشيطانِ، فإذا فَرَغَ فليَلْعَقْ أصابعَهُ، فإنه لا يَدري في أيِّ طَعامه البركة"حديث أنس رواه مسلم. حديث جابر رواه مسلم
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Masud -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah"Abdurrazak Ya Rawaito shi
عن البراء بن عازب –رضي الله عنهما- قال: كانَ رجلٌ يَقرَأُ سُورةَ الكهفِ، وعندَه فَرَسٌ مَربُوطٌ بِشَطَنَيْنِ، فَتَغَشَّتْهُ سَحَابَةٌ فَجَعَلَتْ تَدْنُو، وجَعلَ فَرَسُه يَنفِرُ منها، فلمّا أصبحَ أتَى النبيَّ صلى الله عليه وسلم فَذَكرَ ذلك له، فقالَ: «تِلكَ السَّكِينةُ تَنَزَّلَتْ للقُرآنِ».متفق عليه
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".Muslim ne ya rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"Bukhari ne ya rawaito shi
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai SassarfaBuhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abdullahi Bn Akim -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Tarik Ɗan Ashyam al’Ashja’i, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi yana cewa: Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah.Muslim ne ya rawaito shi